Home Labarai NITDA ta fara horas da matasan NYSC 50 kan noma ta fasahar zamani

NITDA ta fara horas da matasan NYSC 50 kan noma ta fasahar zamani

0
NITDA ta fara horas da matasan NYSC 50 kan noma ta fasahar zamani

 

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa, NITDA, ta fara shirin horas da matasa masu yi wa kasa hidima, NYSC kan shirin Noman a Ƙauye ta hanyar Fasahar Zamani, NASVA.

An fara horon ne a yau Alhamis a Abuja tare da haɗin gwiwar reshen NITDA, mai suna Cibiyar Fasahar Ɗan’adam da Mutum-muti’umi ta Ƙasa, wacce a ka fi sani a turance da National Center for Artificial Intelligence and Robotics, NCAIR, da kuma Rumbun Fasahar Sadarwa na Abuja, ATV.

Horon dai wani ɓangare ne na ayyukan hukumar na tabbatar da cewa a na tafiyar da dukkan sassan kasar nan ta hanyar fasahar zamani.

Kashifu Inuwa, Darakta-Janar na NITDA, ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama tare da nuna sha’awa kan yin sana’a ta hanyar noma.

Inuwa, wanda ya samu wakilcin Salisu Kaka, Daraktan riko na Sashen Bunkasa Tattalin Arzikin ta Fasahar Zamani na NITDA, ya ce dabarun da za a koyar za su baiwa mahalarta taron damar samar da ayyukan yi.

A cewarsa, mahalarta taron za su kuma iya ba da gudummawar kason su don tabbatar da karuwar yawan aiki, samun riba, samar da abinci, da ingantaccen noma.

Shugaban NITDA ya bukace su da su jajirce wajen gudanar da shirin, inda ya kara da cewa zai dauki tsawon watanni shida ana sa ran zai kawo sauyi, sannan a taimaka musu wajen dogaro da kai da samar da ayyukan yi.