
Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta gaggauta janye ƙarin farashin litar man fetur da ta yi a jiya Laraba.
A jiya ne dai kanfanin mai na kasa, NNPCL, ya sanar da karin farashin litar mai daga Naira 898 zuwa sama da Naira 1,000 a fadin ƙasar, lamarin da ya jefa yan kasar cikin damuwa.
Sai dai kuma Daily Trust ta rawaito cewa Ajaero, a wata sanarwa da ya fitar a juya Laraba ya ce gwamnatin na ta kara farashin mai a duk wata yayin da ta gaza ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashi.
Hakazalika, a cewar sa, yanzu an bar kamfanonin mai masu zaman kansu su rika sayar da mai a farashin da su ka ga dama.