Home Labarai NLC ta sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi daga gwamnatin taraiya

NLC ta sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi daga gwamnatin taraiya

0
NLC ta sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi daga gwamnatin taraiya

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi na naira 54,000 da gwamnatin ƙasar ta amince za ta biya.

A tataunawar da ƙungiyar ta yi da kwamitin ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta kafa, kwamitin ya yi tayin biyan naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar.

Hakan ƙari ne a kan naira 48,000 da kwamitin gwamnatin tarayyar ya yi tayin biya a zaman da ɓangarorin biyu suka yi cikin makon da ya gabata.

NLC ta ce ta yi watsi da tayin ne sakamakon halin matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

Ɓangarorin biyu za su sake zama a yau Laraba domin ci gaba da tattaunawar kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

Tun da farko dai NLC ta ce tana so gwamnatin ƙasar ta biya naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, la’akari da halin da ake ciki a ƙasar na ƙaruwar hauhawar farashi da karyewar darajar kudin ƙasar.

BBC Hausa