Home Labarai NLC ta yi watsi da ƙarin farashin man fetur

NLC ta yi watsi da ƙarin farashin man fetur

0
NLC ta yi watsi da ƙarin farashin man fetur

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta yi watsi da sabon farashin man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya kara.

A yau ne NNPC ya umurci gidajen man da ke fadin kasar nan da su sayar da mai tsakanin Naira 480 zuwa 570 kan kowace lita.

Garba Deen Muhammad, Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Kamfanin, NNPC Ltd, ya ce an yi gyaran farashin ne daidai da “hakikanin kasuwa”.

Sai dai shugaban kungiyar ta NLC, Kwamared Joe Ajaero, wanda ya yi wa manema labarai karin haske a yau Laraba a gidan kwadago da ke Abuja, ya ce kungiyar ba za ta amince da hakan ba.

Ya kara da cewa kayyade farashin ba abu ne da gwamnati za ta yi gaban kanta ba.