
Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar ƴan ta’adda ta IPOB, ba ya jin daɗin kashe-kashen da a ke yi da kuma dokar zaman daɓaro da a ka daɗe a na yi a yankin Kudu-maso-Gabas.
Har yanzu dai ƙungiyoyin IPOB ɗin na sanya dokar ta zaman daɓaro a gida, inda su ka yi iƙirarin cewa su na aiwatar da ita ne bisa umarnin Kanu ɗin.
Sai dai Soludo ya ce hakan na daga cikin batutuwan da su ka tattauna shi da Kanu a ziyarar da ya kai wa shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB a wurin da ake tsare da shi a Abuja a jiya Juma’a.
Christian Aburime, mai magana da yawun Soludo wanda ya bayar da sanarwa a yau Lahadi a Awka, ya ruwaito Soludo na cewa Kanu na cikin koshin lafiya.
Sanarwar ta kara da cewa “Kanu yana goyon bayan ci gaba da neman mafita mai dorewa kan rashin tsaro a yankin Kudu-maso-Gabashin kasar nan.”
A cewarsa, “Kanu ya sanar da ni cewa idan aka ba shi dama zai yi wani jawabi ta kafafen yaɗa labarai da zai magance tabarbarewar tsaro a yankin Kudu-maso-Gabas da sunan tayar da zaune tsaye.
“Ya bayyana bakin cikinsa kan abin da ya bayyana a matsayin ‘mummunan kashe-kashe’ na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, garkuwa da mutane da duk wani nau’i na laifuka, ciki har da cin zarafi na sanya dokar zaman daɓaro da wasu kungiyoyi daban-daban ke yi da ke da’awar cewa suna yi ne ko kuma a madadin kungiyar IPOB,” in ji sanarwar.