
Kamfanin mai na kasa, NNPC, ya ce ta na neman kamfanunuwa masu zaman kansu da za su iya ci gaba da rike matatatun mai ta Warri da ta Kaduna.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a shafin sa na X.
Matatar mai ta Warri wacce ke jihar Delta, an kaddamar da ita ne a shekarar 1978 da manufar samar da tattacen mai ga kasuwannin kudu maso yamma da kudancin Nijerya.
Itama matatar mai ta Kaduna, an kafata ne a shekarar 1980 domin samar da tataccen man fetur ga Arewacin Nijeriya
Sai dai matatun sun shafe tsawon lokaci basa aiki.
Matatun dai na iya tace ganga dubu 235 a rana guda.