Home Labarai NNPC ya sa ranar fara haƙar ɗanyen man fetur a Jihar Nassarawa

NNPC ya sa ranar fara haƙar ɗanyen man fetur a Jihar Nassarawa

0
NNPC ya sa ranar fara haƙar ɗanyen man fetur a Jihar Nassarawa

Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC) ya ce a watan Maris mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa.

Gano man a rijiyar Keana+ta-Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.

A cikin sanarwar da ya fitar a jiya Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.”

Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin.

Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lalata muhalli.

“Dole a gaggauta fara aikin nan saboda komai yanzu na sauyawa a duniya. Nan da shekara 10 ba lallai ne kowa ya yarda ya zuba jarinsa a harkar man ba matukar ba ya san zai ci riba ba. Saboda haka idan muka fara da wuri, ina ganin zai fi,” in ji Mele Kyari