
Babban kamfanin mai na ƙasa NNPC ya sanar da aniyarsa ta ƙaddamar da sabbin tashoshin wutar lantarki a Abuja da Kaduna da kuma Kano wanda zasu samar da wuta mai ƙarfin megawat 4600.
Wannan sanarwar ta fito ne daga jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin mai na ƙasa NNPC. Nda Ughamadu, yace wannan abu zai yuwu ne bayan da aka amince da kwantiragin sanya bututun iskar gasa daga Ajakuta zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
kamfanin AKK me aikin sanya bututai ne zai yi wannan gagarumin aiki, wanda babban kamfanin mai na kasa ya sahale masa.
Mista Nda ya ruwaito shugaban kamfanin mai na kasa Maikanti K. Baru yana mai cewar Kamfanin mai na kasa tare da hadin guiwar wasu masu zuba jari ne zasu yi wannan gagarumin aiki aikin shimfida bututun da zai kai ga samar da tashoshin lantarkin.
“Na daga daga cikin tanade tanaden wannan gwamnati domin magance matsalar hasken wutar lantarki, samar da wannan tashoshi a Abuja da Kaduna da Kuma Kano.”
Haka kuma, NNPC zata gina karin sabbin kamfanin samar da takin zamani a wasu sassa na kasarnan, musamman yankin Izzon dake yankin jihar Neja.
Sanarwar ta cigaba da cewar, a bisa tanade tanaden Shugaban kasa Muhammadu Buhari na bunkasa yadda ake tono gurbataccen man fetur a Najeriya. NNPC ta dukufa wajen samar da yanayin da za’a tono gurbataccen man da yake dankare a yankin Bida dake jihar ta Neja.
“Tuni muka gama dukkan wasu gwaje gwajen da wajen da ya kamata ayi aikin tono man, kuma aiki ne da kwararru daga jami’ar Ibrahim Babangida dake Lapai suke jagoranta, kuma muna sa ran kammaluwar wannan aiki cikin watanni uku”
Mista Nda ya cigaba da bayani yana cewar, babban kamfanin mai na kasa zai yunkura wajen karfafawa ‘yan kasuwa guiwa musamman masu zuba jari wajen gina manyan tashoshin manyan motocin dakwan mai a yankin Minna da Suleja da Tagina da Mokwa da sauransu, sannan kuma zasu tabbatar masu amfani da manyan motocin na amfani da sabbin tashoshin da za’a gina.
Haka kuma, NNPC ta gargadi yankunanta na shiyya, da kada su kuskura su dinga zubawa motoci man da ya wuce lita 40,000 wanda bisa ka’ida shi aka amince kowacce mota kada ta dauka fiye da shi.
NAN