Home Siyasa 2023: NNPP ta ƙaryata cewa ta ajiye Kwankwaso ta ɗau Tinubu a Osun

2023: NNPP ta ƙaryata cewa ta ajiye Kwankwaso ta ɗau Tinubu a Osun

0
2023: NNPP ta ƙaryata cewa ta ajiye Kwankwaso ta ɗau Tinubu a Osun

 

 

Jam’iyyar NNPP, reshen jihar Osun, ta musanta rahoton cewa ta amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Shugaban riko na jam’iyyar a jihar, Abdussalam Abdullateef, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Asabar a Osogbo, ya bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da rahoton.

Abdullateef ya ce ƴan jam’iyyar su huɗu, wadanda ake zargin sun amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, “to sun yi wa kansu”.

A cewarsa, ɗan takarar shugaban kasa daya tilo da jam’iyyar NNPP ta sani shi ne Sen. Rabiu Kwankwaso, “wanda ke da duk abin da a ke buƙata na samar wa kasarmu sabuwar rayuwa a nan gaba a ranar 29 ga Mayu, 2023 da ma bayan nan”.

“Mu ƴan jam’iyyar NNPP na Osun muna jaddada goyon bayanmu ga mai girma Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na NNPP.

“Shi ne wanda ya fi cancanta a cikin duk ƴan takarar shugaban kasa a Najeriya, ta fuskar gyara ilimi, gogewar aiki, ingantacciyar siyasa da kusanci ga talakawa,” in ji shi.