
Jam’iyyar NNPP ta bayyana Ladipo Johnson a matsayin wanda zai yi wa ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso mataimaki.
Johnson ya fito ne daga Jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya kuma ya yi takarar kujerar gwamna a jam’iyar.
NNPP ta bayyana hakan ne ta shafinta na Twitter @nnpphqabuja1, wanda kuma sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Manjo Agbor ya tabbatar da hakan.
Jam’iyyar ta rubuta: “Hanyar zuwa 2023: Barisfa Ladipo Johnson shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar mu.”
Johnson wanda shi ne shugaban Cibiyar Ci gaban Kasuwanci da Gudanarwa na Afirka, shi ne kuma ya samar da cibiyar ‘The Johnson Initiative for Positive Impact.’