Home Siyasa 2023: NNPP za ta ƙwaci mulki a hannun Zulum, in ji Kwankwaso

2023: NNPP za ta ƙwaci mulki a hannun Zulum, in ji Kwankwaso

0
2023: NNPP za ta ƙwaci mulki a hannun Zulum, in ji Kwankwaso

 

 

Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar sabuwar jam’iyya ta hamayya, NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa za ta kwace mulki daga hannun gwamna Babagana Umara Zulum a zaɓen 2023.

Kwankwaso ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin bude ofishinsu na kamfen a jiya Asabar.

Sanata Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaɓe a Najeriya tun daga matakin jihohi har Tarayya.

Sannan ya buƙaci magoya bayansa su kasa su kuma tsare kamar yada ya aiwatar a Kano a lokutan zaɓe.

Kwankwaso ya je Maiduguri ne kwana biyu bayan hukumar raya birane ta jihar ta rufe ofishinsu kafin daga bisani gwamna Zulum ya umarci a sake buɗe ofishin.