Home Nishaɗi Nollywood ta shirya fina-finai 340 a watanni hudun ƙarshe na 2022 – NFVCB

Nollywood ta shirya fina-finai 340 a watanni hudun ƙarshe na 2022 – NFVCB

0
Nollywood ta shirya fina-finai 340 a watanni hudun ƙarshe na 2022 – NFVCB

Hukumar tace fina-finai da bidiyo ta kasa, NFVC, ta ce ta karba tare da tantance fina-finai 340 da masana’antar fina-finan kudancin Nijeriya, Nollywood ta shirya a watanni huɗun karshe na 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Adedayo Thomas, Babban Daraktan NFVCB ya fitar ranarJuma’a a Abuja.

Wannan, in ji Thomas, ya haɗa da dukkan fina-finan da aka mika wa hukumar daga sassan kasar.