Home Labarai NSCDC ta samar da rundunar mata ta musamman domin tsaron makarantu 81,000 a Nijeriya

NSCDC ta samar da rundunar mata ta musamman domin tsaron makarantu 81,000 a Nijeriya

0
NSCDC ta samar da rundunar mata ta musamman domin tsaron makarantu 81,000 a Nijeriya

 

 

Babban kwamandan hukumar tsaron fararen hula ta ƙasa, NSCDC Ahmed Audi, ya ce sun samar da rundar mata ta nusamman domin samar da tsaro ga makarantu 81,000 da aka gano suna da barazanar tsaro.

Audi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Abuja.

Ya ce an samar da rundunar matan ne bayan da aka yi nazari sosai kan dukkan makarantun kasar.

“Mun gudanar da gwajin tantance na makarantu masu rauni wanda wani nau’i ne na bincike da muka ba da izini don kawai a sami ƙiyasi na adadin makarantun da muke da su a kasar nan, makarantu nawa ne za mu ce ba su na da cikakken tsaro.

“Tsaro, ma’anar cewa suna da kasancewar tsaro ko na gwamnati na ko kuma na ƴan sa kai? An katange makarantun?

“Bayan da muka yi wannan binciken, mun fahimci cewa akwai matsala a kasar nan ta fuskar tsaro a makarantu kuma tsaro ne, domin bayanan da muka samu masu ban tsoro ne.

“Inda muke da makarantu sama da 81,000 wadanda ba su da cikakken tsaro, babu shinge, babu jami’an tsaro don haka abu ne mai tsanani,” in ji shi.

Ya ce samar da rundunar mata na daya daga cikin matakan da aka dauka, ganin cewa fyade na daya daga cikin munanan illolin sace yara da malamai domin neman kudin fansa.

“Wadannan miyagun mutane suna amfani da fyade a matsayin daya daga cikin dabarunsu kuma ka san idan mace ta ji wani abu game da fyade, ta na daukar abin da gaske kuma ya zama abin damuwa sosai.

“Don haka, a yanzu mun ce, mata ne kaɗai su ka fi cancanta da aikin nan da kuma yin shi da kyau, ita ce mata.

“Sabo da haka mu ka samar da rundunar mata ga musamman wacce sojoji su ka basu horo kuma mun ɗora musu alhakin kare makarantun nan,” in ji shi