
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ta daga likkafar kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, COE Kano, zuwa jami’ar ilimi.
Babban Sakatare na NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, a lokacin da ya ke mika lasisin gudanar da makarantar ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja a jiya Talata, ya ce an amince da jami’ar a matsayin jami’ar jiha ta 61 a fadin kasar nan.
Rasheed ya yi alkawarin baiwa jami’ar goyon baya a fannin ba da shawarwari ɓangaren dabarun gudanarwa don samun damar amfani da kuɗaɗen gudanar wa mai dorewa.
“Ta kwafin wannan wasika, za a sanar da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), TETFUND da NYSC game da kafa wannan jami’a,” inji shi Rasheed
Gwamna Abdullahi Ganduje a lokacin da ya ke karbar takardar, ya bayyana cewa akwai bukatar a samar da sabuwar jami’ar domin rage nauyi a kan jami’o’in jihar.
Gwamna Ganduje ya nuna damuwarsa kan rashin aikin yi ga matasa da su ka kammala karatun digiri masu digiri, wanda ya sa gwamnatin jihar ta kafa wata cibiya ta bunkasa sana’o’i ta biliyoyin nairori mai suna Aliko Dangote kuma ta kaddamar da aikin horar da matasa makonni biyu da su ka gabata.