
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zaɓukan 2023 sun nuna yadda mulkin dimokuraɗiyya ke ci gaba da ginuwa da kuma samun karfi musamman ma ta yadda masu zaɓe suka waye da kuma sanin shugabannin da za su zaɓa.
BBC ya rawaito cewa shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu a fadarsa da ke Abuja, inda ya ce sakamakon zaɓen gwamnoni guda 10 da suka kasa samun nasarar zuwa majalisar dattawa, ya nuna cewa yanzu babu tabbas game da samun mulki kuma yanzu masu zaɓe su ke da wuƙa da nama.
“Hakan ya nuna cewa dimokuraɗiyyar mu na ƙara girma da kuma yadda masu zaɓe suka waye. Abin da ya bani mamaki shi ne ɗan Najeriyar da aka raina, a yanzu shi ke da wuƙa da nama wajen zaɓar wanda ya dace,” in ji Buhari.
“An mayar da cewa bayan gwamna ya yi shekara takwas, daga nan zai tafi majalisar dattawa ba tare da shan wahala ba. Daga yanzu babu wanda zai sake raina mai zaɓe a Najeriya. Siyasa za ta zama abu mafi wahala nan gaba,” a cewar Buhari.
Da yake magana, sabon Sarkin na Dutse, Alhaji Muhamamd Hamim, ya gode wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari saboda taimaka wa jihar Jigawa ta samu ci gaba a ɓangaren noman shinkafa da amincewa da gina layin dogo daga Kano zuwa Dutse da kuma dawo da zaman lafiya a jihar