Home Labarai NYSC: Gwamnatin tarayya ta kara alawus din masu yi wa kasa hidima

NYSC: Gwamnatin tarayya ta kara alawus din masu yi wa kasa hidima

0
NYSC: Gwamnatin tarayya ta kara alawus din masu yi wa kasa hidima

Gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus na wata-wata na masu yinwa ƙasa hidima daga Naira dubu 33 zuwa Naira dubu 77.

An sanar da karin alawus din ne a wata sanarwa da shafin kula da shirin na masu yiwa kasa hidima ya wallafa a Facebook.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus ga masu yiwa kasa hidima zuwa Naira dubu 77 farawa dafa watan Yuli na 2024.

“An dau matakin ne bisa amincewa da dokar mafi karancin albashi ta 2024. Hakan na dauke ne cikin wata wasika daga hukumar kula da albashi ta kasa mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba 2024 wacce Mista Ekpo Nta ya sanyawa hannu.

” Kafin hakan, darakta janar na shirin NYSC, Janar YD Ahmed, ya kai ziyara ga shugaban hukumar kula da albashin inda ya nemi a kara lura da walwalar masu yiwa kasa hidima.”