
Kungiyar lauyoyin Najeriya, bangaren kare muradun jama’a da ci gaban dokar kasa, NBA-SPIDEL, ta bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta kori ministar al’adu da tattalin arziki a fannin nishadantar wa, Hannatu Musawa, daga mukaminta bisa zargin karyar dokar shirin bautar ƙasa, NYSC.
A wata kara mai lamba FCH/ABJ/05/90/2024, NBA ta kuma bukaci kotun da ta tilasta wa hukumar NYSC ta soke takardar shaidar kammala wa da ta baiwa Musawa da shugaban kamfanin waƙa na Kennis Music, Kenny Ogungbe.
A tuna cewa wata kungiyar kare hakkin farar hula mai suna ‘Human Rights Writers Association of Nigeria’ a watan Agustan 2023 ta zargi Musawa da yin hidimar ƙasa bayan kuma ta na matsayin minista.
Hakazalika, a watan Oktoban 2023, shi ma Ogungbe ya wallafa hoton sa sanye da kakin NYSC, inda ya bayyana cewa ya kammala NYSC yana da shekaru 53.
Sai dai hukumar ta NBA, a cewar jaridar Punch, ta yi zargin cewa bayar da satifiket ga ma’aikatan biyu ya saba wa tanadin dokar NYSC mai suna Cap N84.LFN 2024.
Wadanda suka shigar da karar sun hada da Shugaban NBA-SPIDEL, John Aikpokpo Martins, da Sakatariyar NBA-SPIDEL, Funmi Adeogun, yayin da wadanda ake kara suka hada da Musawa, Ogungbe, NYSC, da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya.