Home Labarai Obasanjo ya fadi gaskiya game da Buhari, amma bama tare da shi – Afenifere

Obasanjo ya fadi gaskiya game da Buhari, amma bama tare da shi – Afenifere

0
Obasanjo ya fadi gaskiya game da Buhari, amma bama tare da shi – Afenifere

Daga Hassan Y.A. Malik

Kungiyar kabilar yarbawa ta Afenifere ta nisanta kanta da tafiyar tsohon shugaban kasan Nijeriya, Olusegun Obasanjo wacce ta rikide zuwa jam’iyyar ADC.

Wannan sanarwa dai ta fito ne ta bakin wani jigo a kungiyar, Cif Ayo Adebanjo a yayin da ya ke zantawa da jarin Sun.

Cif Adebanjo ya ci gaba da cewa, kungiyar Afenifere ba ta yi amanna da tafiyar Obansanjo da ya kira CNM da a yanzu suka koma jam’iyyar ADC ba saboda yarda da suka yi cewa shi Obansanjo na daya daga cikin matsalolin kasar nan.

Ya ce, “Su wane ne a bayan wannan tafiyar? Wai kuna nufin Obasanjo? Sam bana tare da tafiyar Obasanjo saboda shi Pbasanjon na daya daga cikin matsalolin kasar nan da ke bukatar a kawar.

“Duk da dai Obasanjo gaskiya ya fada a batun gazawa da gwamnatin Buhari ta yi, amma wannan ba dalili bane da zai sanya mu bi waccan tafiya ta Obasanjo.

“What has Obasanjo accused Buhari of doing that he was not guilty of? Let us look for young, bright men with ideas to organise the country to a better system of government.

“Shi wane abu ne wanda Obasanjo ya zargi Buhari da aiwatarwa da shi ba aikata ba? Kamata ya yi mu nemi matasa masu nini a jika da kuma gogewa a harkokin mulki da gudanarwa don su dawo da kasar cikin hayyacinta.

“Obasanjo na da ‘yancin ya kafa jam’iyya k kuma ya shiga duk jam’iyyar da ya ga dama. Wannan damarsa ce da kundin tsarin mulkin kasa ya tabbatar masa. Saboda ni ba shigarsa ADC ce matsalata ba. Matsala ita ce na gaya muku cewa Afenifere bata da waa alaka da tafiyar Obasanjo.”

Da ya ke magana akan batun ko wai jam’iyyar APC za ta zarce a a shekarar 2019, Adebanjo ya ce, “Jam’iyyar APC rigima ta ke yi a tsakaninta. Babu dimokuradiyya a cikin jam’iyyar. To, ta ya ya jam’iyyar da ta ksa rike kanta za ta rike kasa gaba daya?

“Na fada a na nanata cewa Buhari na kaunar kasar nan kuma da gaske yake kan batun kasancewar Nijeriya kasa daya, abinda ya dace ya yi shi ne ya sauya fasalin kasar nan ta yadda kowace jiha za ta samu gashin kanta in dai da gaske ya ke kasar ce a zuciyarsa ba wai yana da wata boyayyiyar manufa ba,” inji Adebanjo.