
Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da takwaransa na jihar Imo kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya Lahadi a Daura, jihar Katsina.
Sun dai yi wannan ganawa ne da Shugaban kasa, a yayin da ake ta kiran a soke zaben ‘Kwangires’ na jam’iyyar da aka gudanar a mazabun Najeriya baki daya, inda aka samu tashe tashen hankula da dama a yayin zabubbukan a wasu jihohi.
Da yake magana da ‘yan jaridu bayan da suka gama ganawa da Shugaban kasa, Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewar, ya shaidawa Shugaban kasa irin yadda zabubbukan suka fuskanci kalubale da rikici a gurare da dama.
Idan ba’a manta ba, wasu fusatattun matasa sun yi aika aika a sakatariyar jam’iyyar ta APC a jihar Imo, inda nan ce jihar Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC din mai mulki.
“Abinda muke fata shi ne samun kyakkyawar Demokaradiyya ta cikin gida, a baiwa kowanne dan jam’iyya hakkinsa, amma abinda muke gani na kama karya da rashin gaskiya a wasu jihohin dole ya tsaya haka”
A nasa bangaren, Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana cewar “Zaben ya tafi lami lafiya a yankin kudu maso gabashin Najeriya mai fama da rikici” ya kuma kara da cewar, a yankin Arewa maso yamma da ya hada da Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kebbi an yi zaben lami lafiya ba tare da samun wata hayaniya ba.
Sai dai kuma, wasu rahotanni sun nuna cewar wasu jihohin an gudanar da zaben ne kashi biyu a cikin jam’iyyar, yayin da bangarorin da basa ga maciji da juna suka gudanar da nasu zaben kowanne.