
Tsohon mai taimakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Kafafen Sada Zumunta, Reno Omokiri ya ƙalubalanci Mai taimakawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan Kafafen Yaɗa Labarai, Garba Shehu da ya tafi garin Bama na Jihar Borno ya kwana ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba, indai da gaske shugaban ya inganta tsaro a Nijeriya.
A tuna cewa a jiya Juma’a ne dai Garba Shehu, a jawabin da ya yi a bikin cikar Jami’ar Alƙalan ta Katsina shekara goma da kafuwa, ya ce Buhari ya cancanci jinjina sabo da ya samar da tsaro a ƙasar nan.
Kuma Katsina, in da Garba Shehu ya yi jawabin, na fama da rashin tsaro na aiyukan ƴan fashin daji, inda har a ka katse layukan wayar salula a wasu sassan jihar domin yaƙi da ƴan ta’addan.
Da ya ke maida martani ga Garba Shehu, Omokiri ya yi tayin ba shi kimanin dalar Amurka 50,000, kwatankwacin Naira Miliyan 23, matukar hadimin shugaban ƙasar ya kashe dare shi kaɗai a Bama ba tare da rakiyar jami’an tsaro, don bashi kariya ba.
Omokiri ya wallafa haka ne a saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwar da Garba Shehu a shafinsa na kafar sadarwa a yau Asabar.
Haka kuma, Omokiri ya taya Garba Shehu murna tare da yi masa fatan alheri, da fatan samun shekaru masu yawa nan gaba.
Daily Nigerian Hausa