Home Labarai Orubebe ya fice da ga PDP

Orubebe ya fice da ga PDP

0
Orubebe ya fice da ga PDP

 

Tsohon Ministan Ma’aikatar kula da Harkokin Neja Delta a Najeriya, Godsday Orubebe ya sanar da barin jam’iyyar adawa ta PDP.

Orubebe ya sanar da ficewar ne a wasiƙar da ya aike wa Shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, in ji jaridar TheCable.

”Na zaci a lokacin da muka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa a 2015 a wani yanayi mai sarkakiya, jam’iyyar za ta yi amfani da lokacin da take da shi na zamanta babbar jam’iyyar adawa ta lalubo hanyoyin dawowa kan mulki”, in ji Orubebe.

A cewar Orubebe halin da PDP take ciki a halin yanzu ya nuna cewa jam’iyyar ba ta shirya cin zaɓen 2023 ba.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa sunan Orubebe ya yi fice a 2015 a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da ya tada hayaniya a na tsaka da ƙirgen ƙuri’u na zaɓen da Shuagaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya lashe.