
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin bayar da tallafin Nairq dubu goma ga ‘Yan kasuwa a kasuwar Utako dake babban birnin tarayya Abuja.
Ana da ran ‘Yan kasuwa da dama ne zasu amfana da wannan shirin na bayar da tallafi da Gwamnatin tarayya yake yi, domin bunkasa kasuwancin kananan ‘Yan kasuwa.