Home Labarai Zaɓen Osun: Ɗan kungiyar tsaro ta Amotekun ya harbi kansa yayin murnar nasarar Adeleke

Zaɓen Osun: Ɗan kungiyar tsaro ta Amotekun ya harbi kansa yayin murnar nasarar Adeleke

0
Zaɓen Osun: Ɗan kungiyar tsaro ta Amotekun ya harbi kansa yayin murnar nasarar Adeleke

 

 

 

Cikin rashin sani, wani mutum mai suna Sunday Akingbala, wanda aka ce yana goyon bayan jam’iyyar PDP kuma ɗan kungiyar tsaro ta Amotekun ne, ya harbi kansa a lokacin da yake murnar nasarar Ademola Adeleke, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar a Jihar Osun.

An ce harbin ya faru ne a garin Ile Ife a yau Lahadi.

An kai mutumin asibitin Cocin Seventh Day Adventist da ke Lagere, Ile Ife, amma daga baya aka maida shi asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo.

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun, Adeleke, ya samu ƙuri’u 403,371 inda ya doke Gboyega Oyetola, gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 375,027.