Home Labarai Zaɓen Osun: Tun zamanin Awolowo na ke zaɓe ban taɓa fashi ba — Dattijo

Zaɓen Osun: Tun zamanin Awolowo na ke zaɓe ban taɓa fashi ba — Dattijo

0
Zaɓen Osun: Tun zamanin Awolowo na ke zaɓe ban taɓa fashi ba — Dattijo

 

 

Wani dattijo mai shekara 75 da ya fito zaɓe a yau Asabar a Jihar Osun ya shaida wa BBC cewa zaɓe bai taɓa wuce shi ba tun zamanin Awolowo.

Pa Olatunji Ojo wanda ya hallara a wata rumfar zaɓe da matarsa ya bayyana cewa haƙƙinsa ne ya kaɗa ƙuri’a kuma yana jin daɗi a duk lokacin da ya yi zaɓe.

“Tun zamanin Obafemi Awolowo nake zaɓe. Ina jin daɗi sosai idan na yi zaɓe saboda ƴancina ne,” in ji shi.

Pa Ojo na ɗaya daga cikin dattawan da suka fito domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen Osun.