Home Wasanni An yi wa Otamendi fashi a gidansa a Portugal

An yi wa Otamendi fashi a gidansa a Portugal

0
An yi wa Otamendi fashi a gidansa a Portugal

 

A safiyar Litinin ne dai rahotanni daga Portugal su ka baiyana cewa ƴan fashi sun shiga gidan tsohon ɗan wasan Man City, Nicolas Otamendi, su ka yi masa fashi.
Otamendi, ɗan ƙasar Argentina wanda yanzu ya ke taka leda a Benfica da ke Portugal, ya gamu da ibtila’in ne bayan kungiyarsa ta doke Famalicao 4-1 a gasar Premeira.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Benfica ta tabbatar da lamarin, inda ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa a safiyar Litinin ne ƴan fashin su ka shiga gidan ɗan wasan.
Ƙungiyar ta ce ƴan fashin sun tursasa Otamendi da ya buɗe ƙofar gidan nasa, inda bayan ya buɗe, sai su ka kutsa ciki, su ka ɗaure hannuwansa da wuyansa sannan su ka cusa kai cikin ɗakin da matarsa da ƴaƴansa ke kwance.
Bayan sun shiga ɗakin, sai su ka yi awon-gaba da sarƙoƙin gwal da kuma agogunan hannu.
Benfica dai ta baiyana cewa ɗan wasan da iyalinsa na cikin ƙoshin lafiya, inda ta ƙara da cewa ƴan sanda sun fara bincike a kan lamarin.