Home Siyasa 2023: Ba ɓoye-ɓoye, ba zan yi APC a zaɓen gwamna na Ogun ba — Amosun

2023: Ba ɓoye-ɓoye, ba zan yi APC a zaɓen gwamna na Ogun ba — Amosun

0
2023: Ba ɓoye-ɓoye, ba zan yi APC a zaɓen gwamna na Ogun ba — Amosun

 

 

 

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan sake tsayawa takarar gwamnan jihar mai ci, Dapo Abiodun, a zaben gwamna na 2023 ba.

Sai dai kuma Amosun, ƙusa a jam’iyyar APC, ya ce ya na goyon bayan ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, kuma zai yi kokarin ganin ya samu nasarar zama shugaban kasar nan.

Da ya ke zanta wa da BBC Yoruba a yau Litinin, Amosun, wanda yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya, ya ce a maimakon haka, zai goyi bayan dan takarar jam’iyyar Action Democratic Congress, ADC, Biyi Otegbeye.

Ya ce: “Don zaben shugaban kasa, ina tabbatar muku, dama, hagu da kuma tsakiya, muna goyon bayan mutum ɗaya (Tinubu).

“Na yi imani muna goyon bayan mutum daya. A kan zaben gwamna, wannan wasan kwallo ne na daban, ba na tare da can ɓangaren.

“Ba na ɓoye-ɓoye ko na ɓuya a bayan yatsa daya don yin fada. Shi ya sa mutane ke ce mani ‘kada ka ce haka.’ A zaɓen gwamna, ni da magoya baya na, ba ma tare da wancan ɓangaren.” in ji Amosun