
Gwamnonin jihohi 36 na Nijeriya sun ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da wata Babbar Kotun Taraiya ta yanke, wacce ta shure ƙarar da su ka shigar su na ƙalubalantar yankan kuɗin Paris Club na $418 da ga asusun su gwamnatin taraiya.
Kuɗin na biyan bashin kamfanunuwan da gwamnatocin jihohi da Kananan hukumomi su ka ɗauka ne domin yin aikin karɓo kuɗaɗen Paris Club.
A ranar 25 ga Maris ne Babbar Kotun Taraiya da ke Abuja, ta kori ƙarar da gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan su ka shigar a kan Gwamnatin Taraiya kan bashin dala miliyan 480 na Paris Club.
Gwamnonin sun shigar da daukaka karar ne ta hannun lauyoyinsu a wata sanarwa da lauyoyin masu lambar girma ta SAN su biyar su ka sanya wa hannu, waɗanda su ka haɗa da S. I. Ameh, J. S. Okutepa, Dr Garba Tetengi, Ahmed Raji da Olumuyiwa Akinboro.
Gwamnonin sun shawarci al’umma da bankuna na gida da na ƙasashen waje da cewa maganar na gaban kotu, kuma su daina magana da wadanda a ke ƙara a shari’ar.
Waɗanda a ke ƙara a shari’ar da gwamnonin ke nufi su ne Chris Asoluka (da ya ke harkarsa ƙarƙashin suna da salo na NIPAL Consulting Network, Linas International Limited, Joe Odey Agi, (da ya ke harka karkashin suna da salo na Joe Agi, SAN & Associates).
Sauran sun haɗa da Riok Nigeria Limited, Prince Nicholas Ukachukwu, Dakta Ted Iseghohi Edwards, Panix Alert Security Systems Limited, Dakta George Uboh, Ned Munir Nwoko, Prince Orji Orizu da Olaitan Bello.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya kori ƙarar ne kan dalilin cewa ba ta da tushe ballantana makama.
Ekwo ya ce masu ƙarar, da su ka haɗa da Antoni-Antoni Janar na jihohi, da Akanta-Akanta Janar na jihohi basu da ikon shigar da ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/1313/2021 ba tare da yardar gwamnonin su ba.
Ya ce ba su da ikon shigar da ƙarar, duba da sashi na 211 na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999.
“Antoni-Antoni Janar na jihohi ba su da ikon yin gaban kansu su shigar da wannan ƙara.
“Ba wani mataki da za a iya ɗauka idan mai ƙara bashi da ikon shigar da ƙara a bisa doka,” in ji shi.
Ekwo ya ƙara da cewa ƙarar ba ta cikin irin ajin ƙararrakin da Antoni-Antoni Janar na jihohi za su shigar ba tare da amincewar gwamnonin su ba.