
Sen. Obinna Ogba mai wakiltar Ebonyi-ta-Tsakiya ƙarƙashin PDP, a jiya Lahadi ya bayyana cewa jam’iyyar ta cancanci yin rashin nasara a zaɓen 2023 saboda rashin gudanar da al’amura da kwamitinta na koli na kasa, NWC ya yi.
Ogba ya shaida wa wani taron manema labarai a mahaifarsa ta Nkalagu da ke karamar hukumar Ishielu cewa kwamitin na NWC ne ya daɓawa kan sa wuƙa ta hanyar ba da tikitin takarar gwamna ga ‘’dan takarar da bai dace ba’’.
Sanatan, wanda ya rasa tikitin takarar gwamna na jam’iyyar bayan doguwar takaddamar shari’a da kotun koli ta yanke, ya yi gargadin cewa kada kwamitin koli na PDP ya ce zai dakatar da kowane mamba.
“Gaskiyar magana ita ce, tun farko, mambobin NWC ne suka cancanci a dakatar da su, musamman ma daga shugaban jam’iyya na ƙasa.
“Shugaban jam’iyya na kasa ya kasa kawo akwatin zaben sa, ballantana mazaɓa, Karamar hukuma da jihar sa kacokan, kuma abu ne daya ya shafi duk masu makirci da suka bayar da tikitin takara ga mutanen su kadai,” inji shi.
Ogba ya kara da cewa, har yanzu akwai dama ga jam’iyyar ta PDP idan ta gyara kurakurenta domin jama’a na son ta har yanzu.