Home Labarai PDP ta amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a zabi dan takarar Shugaban kasa

PDP ta amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a zabi dan takarar Shugaban kasa

0
PDP ta amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a zabi dan takarar Shugaban kasa
  1. Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ya amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a yi zaben fitar da gwani na ‘Yan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi nan gaba kadan.

An samu rarrabuwar kai tun lokacin da aka ayyana birnin Fatakwal a matsayin inda za a yi zaben fidda dan takara, inda wasu suka nuna cewar matukar aka kai taron birnin Fatakwal su ba zasu halarta ba.

Yayin da a gefe guda, Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike yace muddin aka dauke taron daga birnin Fatakwal to kuwa za a fa ba daidai ba a cikin jam’iyyar.

A cewar Wike wasu ‘Yan takarar Shugaban kasa je suke son a dauke taron daga birnin Fatakwal a maida shi wani wajen domin biyan bukatar kansu.

Sai dai kuma, a Zaman da ta yi a ranar Juma’a Shugabannin jam’iyyar sun amince ayi babban taron jam’iyyar na kasa a birnin Fatakwal din.