
Dan takarar Gwamnan Kano karkashin jam’iyyar PDP Abba K. Yusuf ya auka cikin rudani, abinda ya sanya ya dauko hayar kwararren lauya mai mukamin SAN dan kare takararsa.
A ranar biyu ya watan Oktoba ne a wani yanayi mai cike da ayar tambaya, aka yi wani Abu da aka kira zaben fidda gwani na dan takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP a Gidan Kwankwaso dake kan titin Lugard, kuma aka bayyana Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai kuma, mutumin da aka bayyana cewar ya zo na biyu a wannan zaben, Jafar Sani Bello ya shiga da kara gaban Mai Shariah AT Badamasi yana rokon da kotun ta ayyana shi a matsayin dan takarar PDP sakamakon rashin cika ka’idar da Abba K. Yusuf yayi na shigowa PDP din.
A cewar Lauyan Jafar Sani Bello, ya bayyanawa kotu cewar Abba Kabiru Yusuf ya karya sashi na 8 karamin kashi na 8 da ya bayyana cewar tilas wanda duk ya yiwa jam’iyyar kome ya rubuta wasika zuwa ga Shugabancin mazabarsa domin shaida musu komarsa jam’iyyar, abinda yace Abban bai yi ba.
A saboda haka ya roki kotun da ya ayyana Jafar Sani Bello a matsayin dan takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP sakamakon rashin bin doka da Abban yayi na komawa jam’iyyar.