
Jam’iyar PDP ta taya tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 85 da haihuwa.
Jam’iyar ta taya Obasanjo murnar ne a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran ta, Debo Ologunagba, ya fitar a jiya Asabar.
Ologunagba ya bawa Obasanjo a matsayin shugaba na daban a gurin kishin ƙasa, jajirce wa, hangen nesa da kuma matsayi a duniya.
A cewar sa, Obasanjo ya kasance shugaba mai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro, haɗin , zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.
“a matsayin shi na shugaban soja da ana farar hula, Obasanjo mutum ne da bashi da ƙabilanci kuma ya yarda da haɗin kan ƙasa wacce a ka kafa ta a kan gwadaben dimokuraɗiyya, gaskiya, zaman lafiya, adalci, da kuma bin doka,”
Ologunagba ya tuna cewa PDP, a ƙarƙashin mulkin Obasanjo ta biya dukkanin bashin da a ke bin Nijeriya, sannan ta saka wa ƴan ƙasa kishi domin tashi tsaye a nemi na kai, inda hakan ya haifar da bunƙasar tattalin arziki a kowanne fanni.
A ƙarshe, Ologunagba ya ce PDP na taya Obasanjo murna a wannan lokaci da ya ke bikin cikar sa shekaru 85, inda ya yi addu’ar Ubangiji ya ƙaro masa shekaru masu albarka a gaba.