Home Labarai PDP zata gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnan Kano ranar Litinin

PDP zata gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnan Kano ranar Litinin

0
PDP zata gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnan Kano ranar Litinin

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ya tabbatar da cewar zata gudanar da zaben fidda gwani na dan takarar Gwamnan jihar Kano a ranar Litinin bayan dage zaben da akai da kwana daya a bisa yadda uwar jam’iyyar ta kasa ta tsara.

Tuni dai uwar jam’iyyar ta kasa ta tantance Malam Salihu Sagir Takai da Hafizu Abubakar da Aminu Dabo da Jafar Sani Bello da Sadiq Wali da Abba Yusuf da kuma Ibrahim Little Domin shiga wannan zabe.

Wasu bayanai da Daily Nigerian ta samu ya nuna cewar a cikin wakilan jam’iyyar guda 6,000 Kwankwaso Jagoran jam’iyyar nada mutane 1,500 kacal abinda yake nuna akwai jan aiki a gabansa wajen samun nasarar dan takararsa.

Akwai dai alamun cewar rundunar ‘Yan sanda zata yi amfani da hukuncin kotu wajen tarwatsa duk wani taro da PDP karkashin Rabiu Sulaiman Bichi zata kira a jihar, abinda yake kara nuna rashin tabbas ga Kwankwaso da magoya bayansa.