Home Siyasa Peter Obi ya zama ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar LP

Peter Obi ya zama ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar LP

0
Peter Obi ya zama ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar LP

 

 

 

Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya zama ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar LP.

Ya zama ɗan takarar ne a babban taro da kuma zaben fidda-gwani na jam’iyar da ya gudana a Asaba, Jihar Delta.

Tun da fari, a na tsaka da babban taron, Farfesa Pat Utomi ya janye wa Obi.

A jawabinsa, Utomi ya ce ya janye wa Obi ne sabo da shi matashin ɗan takara ne mai jini a jika da zai kawo canjin da s ke buƙata a ƙasar nan.

Hakazalika ɗaya ɗan takarar, Joseph Faduri, mai shekara 45, ya janye wa Obi.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a makon da ya gabata ne dai Obi ya sanar da ficewar sa da ga jam’iyar PDP.