Home Siyasa PRP ta rusa kanta ta haɗe da APC a Sakkwato

PRP ta rusa kanta ta haɗe da APC a Sakkwato

0
PRP ta rusa kanta ta haɗe da APC a Sakkwato

Yayin da ‘yan watanni ya rage a gudanar da zabukan 2023, daukacin jam’iyyar PDP ta Jihar Sakkwato ya ruguje ta haɗe da jam’iyyar APC a jihar.

Dukkanin matakan jam’iyyar, karkashin dan takararta na gwamna, Sa’idu Muhammad Gumburawa ya narke zuwa jam’iyyar APC.

Wadanda suka sauya sheka sun hada da daukacin ‘yan takarar sanatoci uku na PRP a, da daukacin ‘yan majalisar wakilai, da ‘yan takarar majalisar jiha, da kuma dukkan jami’an jam’iyyar daga jiha zuwa kananan hukumomi.

Jagoran jam’iyyar, wanda kuma shine mai rike da tutar gwamna a jihar, Sa’idu Muhammad Gumburawa, ya sanar da jagoran jam’iyyar APC, Sanata Aliyu Wamakko cewa sun yanke shawarar ficewa daga tsohuwar jam’iyyarsu ne domin bayar da gudunmawarsu wajen ganin nasarar APC a 2023 a jihar.

Ya kuma bayyana cewa duba da halin da al’ummar jihar suka tsinci kansu a karkashin gwamnatin PDP, sun shiga APC ne domin hada kai da shugabanninta sannan kuma su ci zabe a dukkanin matakai domin jihar ta dawo kan martabarta kamar yadda take a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Aliyu Wamakko.

Da ya ke jawabi a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka zuwa APC, Wamakko ya bayyana Gumburawa a matsayin aboki kuma abokin hadin gwiwa na gari.

Ya bayyana farin cikinsa da zuwansa APC tare da bayyana APC a matsayin jam’iyyar duk mai son ci gaban jihar Sakkwato.