Home Kanun Labarai Rabaren Hassan Matthew Kukah ya gargadi Shugaba Buhari

Rabaren Hassan Matthew Kukah ya gargadi Shugaba Buhari

0
Rabaren Hassan Matthew Kukah ya gargadi Shugaba Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Babban limamin darikar Katolika na yankin Sokoto, Rabaren Hassan Matthew Hassan Kuka, ya yi jan kunnen mai zafi ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gyatta salon mulkinsa.

Kukah ya bayyana hakan ne a sakonsa na barka da zagayowar shagulgulan bikin Ista (Easter) da ya fitar ga kafatanin ‘yan Nijeriya.

“Mai Girma Shuagaban Kasa, Ka yi nesa da al’ummar da ka ke mulka.

“Akwai damuwa matuka a tsakakkanin al’ummar kasar na na cewa shugabansu ba ya tare da su a cikin kuncin rayuwar da suke ciki. Ya kamata ka gaggauta nemo hanyoyin da za dawo da alakar da ke tsakaninka da talakawan kasar nan kafin shaidan ya yi amfani da wannan gurbi wajen kunna wutar gaba tsakaninka da su,” a sakon da Rabaren Kukah ya fitar.”

“Wannan lokaci na Isata ba lokaci bane da za a iya kira gama-garin lokaci, domin a tsawon lokacin da ka dauka kana shugabancin Nijeriya, babu wani lokaci da ya ke na gama-gari.”

Kukah ya ci gaba da cewa, Nijeriya ta rarraba ta kowace fuska ta yadda dole mu fara duba ta ina ne muka yi kura-kurai don mu gyatta.

A cewar Kukah, wannan lokaci ne da ya kamaa mu tsaya tsayin daka mu fuskanci kasarmu fuskanta da nufin mu kawo karshen ibtila’in da ke addabarmu.

Kukah ya bayyana takaicinsa kan yadda Buhari ke rayuwa irinta yarima, amma talakan Nijeriya ke cikin kunci sakamakon banbamce-banbamcen addini, yanki da kabila da ke dada ruruwa a mulkinsa.

Kukah ya kalubalanci malaman addinai da zama kamar sauaran mutane wajen nuna banbamci a bayyane sakamakon shiga harkokin siyasa da suka yi.

Wannan lamari na shiga siyasa da malaman addinai suka yi, a cewar Kukah, shi ne ya sanya a yau basu da fada a ji kuma suka rasa karfin gwiwarsu na fadawa gwamnati gaskiya.