
A juya Litinin ne wani kamfanin gas ɗin girki mai suna ‘Second Coming Nigeria Ltd.’ ya rabawa gidaje 800 tukwanen gas masu nauyin kilo 12.5 cike da gas ɗin kyauta a Jihar Enugu.
Wadanda su ka amfana da kyautar sun fito ne da ga Amechi da ke Enugu ta kudu da kuma Agbani da ke Ƙaramar Hukumar Nkanu ta yamma.
Da ya ke jawabi yayin rabon tukwanen gas din, Manajan kamfanin, Ogochukwu Ezeonyigbo, ya ce kyautar wani ɓangare ne na tsarin hidimtawa al’umma na kamfanin.
A cewar Ezeonyigbo, Dakta Basil Ogbuanu, Manajan-Daraktan kamfanin ne ya bada umarnin a raba tukwanen domin a saukakawa masu siyen kayan A jihar.
Ta ƙara da cewa an yi rabon ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar.