Home Labarai RAGE MUGUN IRI: An kama masu baiwa ƴan fashin daji bayanan sirri su 1,000 a Katsina – Gwamna Radda

RAGE MUGUN IRI: An kama masu baiwa ƴan fashin daji bayanan sirri su 1,000 a Katsina – Gwamna Radda

0
RAGE MUGUN IRI: An kama masu baiwa ƴan fashin daji bayanan sirri su 1,000 a Katsina – Gwamna Radda

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya baiyana cewa ƴan banga na CWC da ke aikin samar da tsaro a jihar sun kama mutane 1, 000 da ke aikin kaiwa ƴan fashin daji bayanai.

Acewar Gwamnan, nasarar na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da kuma ganin an bunkasa fannin noma a jihar.

Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da Babban Hafsan Sojin Sama, Hassan Abubakar ya kai masa inda ya bayyana alfanun alaka tsakanin rundunar sojin sama da gwamnatin jihar wajen magance ayyukan ‘yan fashin daji.

Ya tabbatar wa rundunar sojin goyan bayan jihar a kokarin da ake yi ta kowacce fuska.

Gwamna Radda ya bayyana nasarorin da aka samu da yadda aka kama masu baiwa ‘yan ta’adda bayanai.

Ya kuma ce gwamnati ta gana da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin jihar don kawar da ‘yan ta’adda.

Bugu da kari, Gwamnan ya ce rashin aikin yi da jahilci da matsin rayuwa na daga cikin abubuwan dake haifar da matsalar tsaro a jihar.