
‘Yan gudun hijira a jihar Neja sun rasa matsugunansu inda, aka barsu da zama cikin mawuyacin hali, ‘yan gudun hijira a jihar Neja na mutuwa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, wanda a ke fi sani da maleriya, saboda rashin hadin kai daga gwamnati da masu ruwa da tsaki. A cikin wannan rahoto, Hamzat Ibrahim ya bayyana yadda ‘yan gudun hijira ke kara fuskantar barazanar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma yadda suke wa kansu magani.
Daga Hamzat Ibrahim Abaga
Babu wanda zai bada labarin wahalar fiye da Lado Pada Bulus, wani matashi mai matsakaicin shekaru, wanda ahalinsa suka mayar da sansanin gudun hijirar Gwada kamar gida. Hare-haren Boko Haram ne ga tilasta musu barin ƙauyensu a shekarar 2019. Bulus da iyalansa sun nemi agaji na wucin-gadi daga sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada, a Ƙaramar Hukumar Shiroro, jihar Neja.
Kwatsam, ba zato ba tsammani, ibtila’i ta faɗa musu Inda ‘Ya’yansa mata biyu, Favor,yar watanni 15, da Victoria, ‘yar watanni 18, suka kamu da zazzabin cizon sauro, kamar yadda zazzabin cizon sauro ta saba kamasu a baya ya yi tunanin za su warke su tashi. Mako guda bayan sun kamu da cutar suka rasa ransu.
“Na kai ‘ya’yana wani asibiti mai zaman kansa da ke Gwada saboda babu ma’aikatan lafiya a sansaninmu Bayan mun yi jiyya na farko, dole ta sa mu ka dawo gida tunda ba ni da kuɗin ci gaba da jiyyar su. Mun bar asibitin muka koma jiyya a gida sai dai bayan mako guda, ’ya’yana duka biyu su ka mutu,” cewar Bulus cike da alhini.

Wannan lamarine mai wuyar mantawa, Bulus wanda a yanzu shi ne shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada, ya koka kan yadda ‘yan gudun hijirar ke fama da karancin abinci a jihar. Ya kasance shugaba tun shekarar 2020, kuma har yanzu lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘ya’yansa mata nacigaba da yaduwa a sansanin.
“A duk lokacin da muke buƙatar kulawar likita, mukan rasa madafa sai dai mu tallafawa junan mu. Kwanan nan, wata dattijuwa ta sake mutuwa a sanadin zazzabin cizon sauro da kuma sauran abubuwan da suka shafi lafiya. Mun kira likita ya duba ta, amma abin takaici,rai ya yi halinsa. Ba mu da isassun kuɗin da za mu kai ta asibiti, munyi iya kokarin mu da dan kuɗin da muke da su,” inji shi.
Halin da Bulus yake ciki da sauran ‘yan gudun hijiran da ke Gwada hakan na nuni da matsalar tsaro da ta addabi jihar Neja, sannan ya kara bayyanar da matsalar rashin kulawa da kiwon lafiya da aka yi watsi da ita, musamman wajen magance cututtuka irin su zazzabin cizon sauro da taifot a sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke fadin jihar.

Rashin tsaro, ‘yan gudun hijira da matsalar zazzabin cizon sauro a jihar Neja
Yayin da rashin tsaro ke kara kamari a Najeriya, kimanin mutane 150,380 ne suka rasa matsugunansu a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, a karamar hukumar shiroro kadai kimanin mutane 27,678 ne suka rasa matsugunansu.
Rikicin ya tilastawa mazauna yankin da dama zama a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin kananan hukumomin jihar.
Matsalar rashin tsaro a jihar Neja na ci gaba da ta’azzara a kullum. Masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da kuma ‘yan ta’adda suna kashe mutane da raunata su tare da sace su.
Sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gwada na daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira uku da aka amince da su a hukumance (sansanin Kuta da Zumba) a karamar hukumar Shiroro wanda hakan ya sa samun kulawa ta bangaren kiwon lafiya ya zama babban kalubale a tsakanin ‘yan gudun hijirar a yankin.
Binciken da wannan jarida ta yi ya nuna cewa duk da shirye-shiryen yaki da zazzabin cizon sauro da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki, nauyin cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtukan ya fi ta’azzara a tsakanin mata da yara a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke yankin karamar hukumar Shiroro.

Cutar: Malaria
Zazzabin cizon sauro cuta ce da ke barazana ga rayuwa, matsananciyar cuta ce da ke yaduwa ta hanyar cizon sauro ta mace mai dauke da cutar Anopheles, nau’in da ya fi yada cutar ga mutane a yankin kudu da hamadar sahara.
Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan mace-macen zazzabin cizon sauro a duniya, kamar yadda rahoton zazzabin cizon sauro na duniya na shekarar 2020 ya nuna, an bayyana cewa ana asarar sama da dalar Amurka biliyan 1.1 (N645.7bn) a duk shekara domin rigakafin zazzabin cizon sauro.
A bisa tsarin dabarun yaki da cutar zazzabin cizon sauro na kasa (NMSP), tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015, yara ‘yan kasa da shekaru biyar sun kai kimanin kashi 62 cikin dari da ke wahala sakamakon cizon sauro sannan kuma kashi 72 cikin dari na mace-mace masu alaka da zazzabin cizon sauro a kasar.An bayyana cewa a cikin shekarar 2021 sama da ‘yan Najeriya 200,000 ne suka mutu sakamakon cutar.
Cutar zazzabin cizon sauro ta yi kamari a jihohin arewacin Najeriya kamar jihar Neja kuma hakan yana ba da gudummawa ga yawan mace-macen jarirai da ‘yan kasa da shekaru biyar a cikin kashi 85 da kashi 106 a cikin 1000 da aka haifa. Yayin da cutar ke kara yaduwa duk shekara,akalla yara 19,000 ‘yan kasa da shekaru biyar ne ke mutuwa a duk shekara a jihar sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, lamarin da ya sa jihar ta zama jihar da ta fi kowacce yawan mace-macen yara kanana sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.
Ka’idojin gano cutar zazzabin cizon sauro na jihar Neja, wanda aka sabunta a watan Disamba 2017, ya bayyana cewa duk wanda ake zargi da kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro dole ne a tabbatar da shi ta hanyar gwajin gaggawar gano cutar (RDT) ko ta hanyar amfani da na’urar gano kannanun halittu( microscopy-)sannan ayi amfani da maganin haɗin gwiwa na tushen artemisinin. ACT).

Duk da wannna abu ne na a yaba,sai dai hakan na kara ta’azzara farashin neman lafiya, wanda galibi yake tsadan samuwa Ga mutanen karkara marasa galihu. Sakamakon rashin kyawun rayuwa da tsaftar muhalli a galibin sansanonin ‘yan gudun hijira, mazauna sansanin sun fi fuskantar kamuwa da cizon sauro.
Teni yanzu tana zaune a sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada,Ta ce ta rasa ‘ya’yan ta biyu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.
“Ya kamata gwamnati ta kawo mana agaji,Babu kudin siyan magani ko kudin kai mara lafiya asibiti kuma, babu ma’aikatan lafiya da za su ba mu taimako a sansanin.
“Mun gudo nan ne saboda ‘yan bindiga da Boko Haram da suka addabi kauyukan mu.”
Tsananin rayuwa da sauran labarai masu ban takaici daga sansanin ‘yan gudun hijirah.
Shekaru uku ke nan da Bulus da ire-irensa suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada, inda suke ci gaba da kokawa kan halin kuncin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki, inda ya nemi da a gaggauta mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa kauyukansu, Bulus ya ce: “Don Allah gwamnati ta ba mu dama mu koma gidajenmu muna shan wahala a nan, ba mu da isasshen abinci kuma ba za mu iya noma ba, ya kamata gwamnati ta bar mu mu koma garuruwanmu, kusan shekara uku kenan da zuwan mu wannan sansanin, abinci kawai muke samu daga gwamnati, wani lokaci sau daya a kowane wata uku, kawai gwamnati ta cika mana rumbunan mu da isassun kayan abinci da sauran kayayyaki, mun godewa Allah, kungiyoyi masu zaman kansu suma sun kawo mana agaji. .”
Habibu Musa shi ne jami’in cigaban sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada ya bayyana yadda barkewar cutar kwalara a sansanin, sakamakon rashin tsafta da samun ruwa mai inganci, ya kashe mutane uku a watan Disamba a shekarar 2021.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, isassun kayan gyaran bayan gida shine mafita wajen rigakafin cututtukan da rashin tsaftar muhalli ke haifarwa. Wadannan kayan gyaran bayan gida suna iya taimakawa wajen toshe fitar kwari da kyankyasai wanda sune ke dauke da cutar da ke yaduwa cikin gidaje.
Wata ‘yar gudun hijira a sansanin, mai suna Maryam Kabiru, ta bayyana cewa: “Mutanen mu sun fara komawa kauyukanmu, amma babu ta inda za mu iya shiga kauyen. Ko jiya ma wasu daga cikin mazajenmu da kannensu da suka je gona har yanzu ba su dawo ba,Ba mu san inda suke ba. Mun rikice ba mu san yadda za mu yi da rayuwarmu ba.
“Muna bukatar gwamnati ta taimaka mana da abinci da magunguna da sauran kayan masarufi.A da ya’yanmu suna makaranta, amma tunda muka yi gudun hijira ba su sake zuwa makaranta ba don haka muna roko gwamnati ta zo ta kawo mana dauki”cewar Maryam.
Masana, gwamnatin jihar Neja sun mayar da martani
A wata tattaunawa ta wayar tarho, daraktan kula da lafiyar jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Neja, Dr. Ibrahim Idris, ya bayyana cewa ‘yan gudun hijirar da tuni suka gaji da zama a sansanonin su sannu a hankali sun fara komawa gidajensu inda a can za su iya samun magunguna cikin sauki.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar tare da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, tana bayar da muhimman kayayyaki ga wadanda abin ya shafa a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban a fadin jihar.
“A dangane da bukatunsu na kiwon lafiya (IDPs), gwamnati ta umurci sansanonin ‘yan gudun hijira da su rika neman ma’aikatan kiwon lafiya a duk inda suke, ko kuma su ziyar ci karamar cibiyar kiwon lafiya (PHC) da ke kusa da su domin gwamnati ba za ta iya gina cibiyar lafiya saboda su ba, domin zaman su a wurin zama ne na wucin gadi,” in ji Idris.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta hannun kungiyar kula da lafiyar haihuwa da lafiyar iyali (ARFH) wacce ke karkashin hukumar yaki da zazzabin cizon sauro ta kasa (NMCP) a jihar Neja, ta dora nauyin gudanar da ayyukanta kamar kula da cutar zazzabin cizon sauro ta hanyar samarwa da kuma bin diddigi cikin gaggawa,gwaje-gwajen bincike (RDTs) da magungunan haɗin gwiwar artemisinin (ACTs), sadarwa,mai ba da shawara, da ƙarfafa zamantakewa da tsarin kiwon lafiya ta hanyar haɓaka iya aiki, saka idanu da kididiga.
A cewar shugaban sashen yada labarai na NSEMA, Ibrahim Hussain, tare da goyon bayan masu ruwa da tsaki suna taimakawa ‘yan gudun hijirar da wajen zama tare da dakile illar ‘yan fashin a kansu.
“Don haka duba da adadin mutanen da ke sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar, ba abu ne mai sauki gwamnati ta iya biya musu dukkan bukatunsu ba. Ciwon da ya zama ruwan dare tsakanin yaran da ke sansanin ‘yan gudun hijira shi ne zazzabin cizon sauro, saboda haka gwamnati ta samar da gidajen sauro da aka yi musu feshin magani, tare da bayar da agajin jinya ga wadanda abin ya shafa.”
Da yake mayar da martani kan sakamakon binciken da aka samu daga wannan rahoto, Haruna Sani, wani ma’aikacin lafiya, ya shawarci masu karamin karfi musamman mata da yara da kuma tsofaffi da su yi taka-tsan-tsan tare da yin amfani da matakan kariya da suka hada da yin amfani da gidan sauro mai dauke da magani da kuma maganin kwari.
Mohammed Al-amin, kwararre a fannin lafiya daga Lapai, ya jaddadawa ‘yan gudun hijirar da su rika kiyaye tsaftar jikinsu domin hana barkewar annoba.
Al-amin wanda ya nuna rashin jin dadinsa ga marasa galihu a sansanin, ya kuma umurci ‘yan gudun hijira da su yi amfani da matakan kariya da suka hada da amfani da gidajen sauro masu dauke da magani da kuma tsaftace muhalli.