Home Labarai Ramadan: Gwamnatin Kano ta yi kakkausan gargaɗi ga masu yin ƙanƙara da gurɓataccen ruwa

Ramadan: Gwamnatin Kano ta yi kakkausan gargaɗi ga masu yin ƙanƙara da gurɓataccen ruwa

0
Ramadan: Gwamnatin Kano ta yi kakkausan gargaɗi ga masu yin ƙanƙara da gurɓataccen ruwa

 

Hukumar Kare Hakkin mai Sayen Kaya ta Jihar Kano, CPC, ta ce ba za ta saurarawa duk wanda a ka samu ya na haɗa ƙanƙara da gurɓataccen ruwa ba, musamman a watan azumin Ramadan.

Shugaban Hukumar, Janar Idris Bello Danbazau (mai ritaya) ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ofishin sa.

Danbazau, wanda Daraktan kula da Aiyuka na Hukumar, Dr.
Tijjani Jafaru ya wakilta, ya ce sun fahimci a lokacin azumin a na haɗa ƙanƙara da gurbataccen ruwa, wanda kuma yin hakan ya saɓa wa dokokin hukumar.

Ya ce sun samar da wani kwamiti mai karfi, wanda zai gudanar da bibiyar yadda ma su sayar da kayan abinci da kayan sha za su gudanar da harkokin su lokacin Azumin Ramadana.

“Bayan Amfani da gurɓataccen ruwa, a kwai kuma waɗanda su ke gudanar da yin ƙanƙara a wuri da yanayi maras tsafta. Kuma su kansu waɗanda su ke kula da wajen, duk waɗannan baza mu saurara musu ba”. Inji Danbazau

Janar Danbazau ya kuma buƙaci al’umma da su riƙa sanar da Hukumar duk wani wajen da su ka ga a na haɗa wa da sayar da kayan cikin ƙazanta da kuma inda a ke tauye mudu da sayar da gurɓatattun kaya, musamman Kayan lemo ko kayan marmari.