
Ƙungiyar Ƴan Tifa ta Jihar Kano ta raba kayayyakin abinci, har da ma tufafi ga ƴaƴan ƴan ƙungiyar da su ka rasu sama da guda 100 a yau Litinin a ofishinta a jihar.
Hakimin Ƙaramar Hukumar Garinmallam, wanda ya samu wakilcin Wazirin Garin malam Sheik Abubakar Rabo Abdulkarim, shine ya jagoranci rabon kayan.
Sheikh Abdulkarim ya ce sanya farin ciki a zuƙatan marayu da taimaka wa rayuwarsu abu ne wanda zai inganta rayuwar su, tare da kawar musu da tunanin rashin iyayen su.
Ya bayyana cewa halin da marayu da iyayen su suke ciki abune na a tausaya musu, musamman yadda su ke kwana babu abinci da kuma yadda ba sa iya zuwa makaranta.
Shi ma a nasa jawabin, Dattijon Kungiyar Alhaji Ali Babba Dan’Agundi, ya ja hankalin ƴaƴan kungiyar Tifa na Jihar Kano da su cigaba da kawo aikin cigaba a kungiyar, tare da ɗaukar nauyin marayun da a ka mutu anka barsu, musamman marayun ‘ya’yan kungiyar.
” Wannan matakin da ku ka ɗauka matakine da zai taimaka muku kuma ya ƙara kauna a tsakanin ku, kuma irin wannan aikin na daga cikin aiyukan da Allah ya ke so, wato taimakawa marayu,” in ji shi.
Tunda fari, a jawabin da ya gabatar na makasudin tallafain Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘yan Tifa na Ƙasa, Kwamared Mamunu Ibrahim Takai, ya ce sun zaɓi marayu 101 da iyayensu ke sana’ar yashi, ƙasa da dutse domin basu tallafin.
“Mun tallafawa Waɗannan Yara ne sakamakon yadda su ka rasa mahaifansu, kuma mun fahimci su na buƙatar taimako tunda muma wata rana za mu koma ga mahaliccimmu kuma za mu so muma a kula da ƴaƴanmu”. Inji Mamunu.