Home Ƙasashen waje Ramadan: Saudiya ta hana limamai yin doguwar addu’ar al-ƙunut a yayin sallar tahajjud

Ramadan: Saudiya ta hana limamai yin doguwar addu’ar al-ƙunut a yayin sallar tahajjud

0
Ramadan: Saudiya ta hana limamai yin doguwar addu’ar al-ƙunut a yayin sallar tahajjud

 

Ma’aikatar Harkokin Addini ta Saudiyya ta jaddada wa limamai a masallatan ƙasar da ke jan sallar dare ta tahajjud da su daina tsawaita addu’o’in Al-ƙunutu don sauƙaƙa wa masallata, a cewar rahoton Saudi Gazette.

Rahoton ya ce an nemi limaman su kammala sallar da wuri kafin kiran sallar asuba don mutane su samu isasshen lokaci tsakanin sallolin biyu.

Kazalika, ma’aikatar ta umarci dukkan masallatai su yi aiki da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. game da addu’ar da aka ruwaito yana yi yayin addu’ar Ƙunutu.

“Ma’aikatar ta nemi limamai su guji tsawaita addu’o’i har ma su mayar da su matsayin huɗuba. Kuma ya kamata su guji zuzuta murya da kuma yin ƙafiya, ana so su yi addu’a cikin ƙanƙan-da-kai da kuma tawalu’u,” in ji rahoton.