
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewa dan wasan baya na Real Madrid Sergio Ramos yazama dan risilin kuma fitar Salah ce tasa sukayi rashin nasara akan kungiyarsa.
Kusan za’a iya cewa wasu kwallaye biyu da aka zura a ragar Liverpool laifin mai tsaron ragar kungiyar ne amma kuma ana alakanta rashin nasarar kungiyar da fitar dan wasa Muhammad Salah kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Klopp yace duk da ciwon da Salah yaji yayi kokarin yaci gaba da buga wasan amma kuma ciwon bazai barshi ba kuma dole yafita yana kuka wanda abin bakin cikine ga dan wasan ga Liverpool da kuma kasar Masar.
Mai koyar da kungiya yaci gaba da cewa Real Madrid tayi kokarin yin amfani da fitar Salah domin su fara kai musu hari amma kuma daga baya sai suka sake nutsuwa bayan da hankalin yan wasan kungiyar ya tashi saboda fitar gwarzon dan wasan.
Sai dai bayan tashi daga wasanne hukumar kula da kwallon kafar kasar Egypt ta bayyana cewa dan wasan buguwa kawai yasamu a kafadarsa kuma suna saran zai samu damar zuwa gasar cin kofin duniya a wata mai kamawa.