Home Kasuwanci Ran ƴan Nijeriya ya ɓaci sabo da kamfanonin Samsung da iPhones na kawo sabbin wayoyi ba caja

Ran ƴan Nijeriya ya ɓaci sabo da kamfanonin Samsung da iPhones na kawo sabbin wayoyi ba caja

0
Ran ƴan Nijeriya ya ɓaci sabo da kamfanonin Samsung da iPhones na kawo sabbin wayoyi ba caja

 

 

 

 

Wasu masu amfani da wayoyin hannu a Nijeriya sun nuna ɓacin ransu game da sabon salon da kamfanonin waya ke yi na cire caja da na’urar jin magana a kunne daga sabbin wayoyi.

Wannan al’amari ya na janyo wa masu amfani da wayar karin kuɗi domin duk wanda ba shi da tsohuwar cajar sai ya fara neman na’urar caja ta asali da zai saya bayan ya sayi sabuwar waya.

Apple ya fara irin wannan salon a cikin 2020 tare da iPhone 12, ya na ambaton dalilan illa ga muhalli. Kamfanin ya ce matakin cire caja da na’urorin kunne daga fakitin wayarsa zai taimaka wajen rage sharar robobi.

Hakanan Samsung ya bi sawun ta hanyar sakin jerin S21 ba tare da caja da abin kunne ba ⅞ 000 irin

Ana siyar da sabuwar iPhone 14 da kuma Samsung S22 ba tare da caja ko abin kunne ba.

Ƴan Nijeriya da su ka shiga shafin yanar gizo na Twitter, suna nuna rashin jin dadinsu da kashe makudan kudade bayan sun sayi wayoyin da farashinsu ya wuce gona da iri, sun ce nan ba da jimawa ba sauran kamfanonin kera wayoyi za su kwaikwayi yanayin idan ba a yi wasa ba.
.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ko a watan jiya ma gwamnatin ƙasar Brazil ta haramta sayar da wayoyin iPhone da ake jigilar su ba tare da caja ba. Wannan shawarar ta zo ne shekaru biyu bayan Apple ya daina haɗa wa da caja da na’urar kunne a cikin kwalayen sayar da iPhone don rage su da rage matsalar yanayi.

Wani umarni da ma’aikatar shari’a da tsaron jama’a ta Brazil ta buga ya kuma lura cewa ana ci tarar kamfanin dala miliyan 2.34 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 12.275.