
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
A ranar Asabar za’a fara buga gasar firimiya ta qasa bayan tafiya hutun kusan watanni uku, qungiyar qwallon qafa ta Plateau United c eta lashe gasar da aka kammala a watan Nuwamban shekarar data gabata.
Qungiyar qwallon qafa ta Kano Pillars zata fara kece raini da qungiyar qwallon qafa ta Katsina United a garin Katsina a ranar Asabar din yayinda mai kare kambu Plateau zata kai ziyara Nasarawa United domin fara kambunta.
Qungiyar qwallon qafa ta Abia Warriors wadda mai koyarwa Rafael Everton, dan qasar Brazil yake jagoranta zata kece raini da wadda ta qare a mataki na biyu a gasar data gabata wato MFM.
El-kanemi ta qasar Maiduguri zata kai ziyara jihar Rivers domin fafatawa da qungiyar qwallon qafa ta River United yayinda qungiyar Heartland ta jihar Imo wadda ta hawo gasar wannan shekarar zata karbi baquncin Sunshines Stars na garin Akure.
Gayadda wasannin zasu kasance a satin wasa na farko
Kwara United vs Niger Tornadors
FC Ifeanyi Uba vs Yobe Desert Stars
Wikki Tourists vs Go- Round FC
Akwa United vs Rangers International
Lobi Stars vs Enyimba International
Heatland vs Sunshine Stars FC
Katsina United vs Kano Pillars
Nasarawa United vs Plateau United
Rivers United vs El-Kanemi Warriors
Abia Warriors vs MFM FC
Za’a buga wasannin a ranakun yau Asabar da kuma gobe Lahadi a filayen wasanni daba-daban dake fadin tarayyar qasar nan.