Home Kanun Labarai Ranar Demokaradiyya: Batutuwan da Shugaban kasa ya tabo a jawabinsa

Ranar Demokaradiyya: Batutuwan da Shugaban kasa ya tabo a jawabinsa

0
Ranar Demokaradiyya: Batutuwan da Shugaban kasa ya tabo a jawabinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayiwa ‘yan Najeriya jawabin ranar Demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar Demokaradiyya, kuma Shugaban yake cika shekaru 3 cif a kan karagar Shugabancin wannan kasa.

A cikin jawabin nasa, SHuaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar lallai anci nasarar karya lagon kungiyar Boko Haram a hare haren da take kaiwa a yankinArewa maso gabashin Najeriya. Duk kuwa da cewar Shugaban ya kaucewa bayyana cewar an gama da Boko Haram.

Shugaban ya kuma bayyana cewar a zamaninsa anci nasarar kwato ‘yan matan Chibok 106 da Boko Haram suka sace su, da kuma ‘yan mata 104 da aka ci nasarar kwato su da Boko Haram din suka sace a makarantar ‘yan mata ta Dapchi dake jihar Yobe, da kuma wasu karin mutane 16,000 da aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram.

Haka kuma, Shugaban ya tabo batun da ya dami mutane da yawa a kasarnan, shi ne batun masu yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma batun rikicin da yaki ci yaki cinyewa na tsakanin Manoma da kuma Makiyaya, wanda ya janyo hasarar rayuka masu dumbin yawa musamman a yankin Binuwai da Taraba da Adamawa.

Bayan nan kuma, Shugaban yayi bayanin yadda aka samu zaman lafiya a yankin Neja Dalta mai arzikin man fetur, inda yace ana samun cigaba wajen samar da zaman afiya a yankin, domin samun adadin man da ake bukata a kullum domin samarwa da Gwamnatin Najeriya kudaden shiga.

Sannan kuma, Shugaban yayi bayanin irin dumbin kudaden da Gwamnati ta tara a tsarin asusun nan na bai daya wato TSA, inda yace anci nasarar tara sama da Naira biliyan 200 wajen kudaden da ake baiwa ma’aikatan bogi, da kuma dawo da zunzurutun kudi Naira biliyan 500 daga hannun masu handama da babakere.

Shugaban ya tabo batutuwa da dama a cikin jawabin nasa. Zamu cigaba da gutsuro muku muna kawowa.