
Jam’iyyar hamayya ta PDP ta zargin kalaman Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar babu komai a cikinsa sai ci da buguzum da alfahari da kuma kambama kai da nuna isa, bayan an gaza bayyana abubuwan da suka damu ‘yan Najeriya da kuma matsalolin da suke damun ‘yan Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, inda yace tun da Shugaba Buhari ya hau karagar mulki bai taba yin jawabin da yake cike da abin kunya irin wannan ba.
A cewababbar jam’iyyar adawar ta Najeriya, wannan jawabin da Shugaban kasa ya gabatar, cike yake da shaci fadi, da bayanin abubuwan da ba haka suke ba, mai makon gayawa ‘yan Najeriya gaskiya, da kuma yin alfahari da ayyukan da sam ba su suka yi su ba.
Kadan ne daga cikin ‘yan Najeriya suka kalli wannan jawabi na Shugaban kasa, kasancewar gazawarsa wajen samar musu da hasken wutar lantarkin da zata basu damar ganin jawabin da aka yi da sassafe.
A cikin jawabin na Shugaban kasa ya kasa jajantawa ‘yan Najeriya abubuwan da suke damunsu musamman na masifu da bala’o’in da sakacin Gwamnatinsa suka janyo su, musamman yawan kashe kashe a yankin Birnin-Gwari na jihar Kaduna da kashe kashen mutane babu gaira babu dalili a jihohin Taraba da Adamawa da Yobe da Borno da Binuwai da Zamfara da Kogi.
Babu wani tabbacin samun kyakkyawa kuma ingantacciyar rayuwa da Shugaban kasar ya baiwa ‘yan Najeriya a cikin jawabin nasa. Duk wannan jawabin yana kunshe ne a cikin kunshin sanarwar da jam’iyyar PDP din ta fitar a yau.
Ko meye ra’ayinku kan wannan jawabi na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP?