
Mawaƙiya ƴar ƙasar Amurka, Cardi B, ta gwangwaje mijinta mai suna Offset da kyautar kuɗi, wuri na gugar wuri har dala miliyan 2 domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Cardi B, wacce ta ke da ƴaƴa 2, ta wallafa fefen bidiyo da ke nuna lokacin da ta ke danƙawa rabin ran nata cekin kuɗin a sahfinta na instagram.
“Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka”, ta rubuta a saman fefen bidiyon.
“Ya zama mallakin sa”, ta ƙara da cewa.
Ta ƙara da cewa ta bashi wannan maƙudan kuɗaɗe ne saboda tansan ya na da harkokin kasuwanci da dama.
Ba wannan ne karo na farko da Cardi B ke gwangwaje mijinta da kyauta ta-gani-ta-faɗa ba.
Ko a watan Oktoba na 2019, mawaƙiyar ta baiwa mijin nata cekin kuɗi na dala dubu 500.
A shekarar 2017 ne dai Cardi B da Offset su ka yi aure cikin sirri, inda su ka yi bikin auren a ɗakin su a birnin Atalanta.