
A yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 14 ga watan Satumba domin sauraron karar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya shigar kan jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Mai shari’a Ahmed Mohammed ya tsayar da ranar ne bayan da ya bayar da sanarwar kara wa’adin da lauyoyin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato da Atiku, Prisicila Eje suka shigar.
An amince da bukatar ne bayan da lauyan masu ƙara, Wilfred Okoi ya ƙi sukan ƙorafin a kan hakan.
Michael Ekamon da Wike sune masu shigar da kara na 1 da na 2 bi da bi a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/782/2022 wacce a ka rubuta a ka kuma shigar aka shigar a ranar 3 ga watan Yuni.
Yayin da PDP ke zama ta 1 da ake kara, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Tambuwal da Atiku na 2 zuwa 4 a kararrakin.
Okoi ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar PDP da Tambuwal da Atiku sun ba shi takardar amsar ƙorafin da ya shigar a gaban kotun.
Wike, a cikin ƙarar, ya nemi da kotun ta ayyana shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Wike ya zo na biyu bayan Mista Atiku a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.
Tambuwal, wanda shi ma dan takarar shugaban kasa ne, ya janye wa Atiku takarar ne karshen lokaci.
Ko da yake Gwamna Wike, a kwanakin baya, ya musanta shigar da kara a kan jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, jam’iyyar da sauran su sun samu wakilci a kotu, sai dai lauyan INEC, wanda bainje kotun ba.