Home Lafiya RANAR YAƘI DA SIDA TA DUNIYA: Masu ɗauke da cutar ƙanjamau 35,000 ke karɓar magani a Kano — Gwamnati

RANAR YAƘI DA SIDA TA DUNIYA: Masu ɗauke da cutar ƙanjamau 35,000 ke karɓar magani a Kano — Gwamnati

0
RANAR YAƘI DA SIDA TA DUNIYA: Masu ɗauke da cutar ƙanjamau 35,000 ke karɓar magani a Kano — Gwamnati

 

 

Gwamnatin Kano ta sanar da cewa masu ɗauke da cutar sida, wacce a ka fi sani da ƙanjamau 35,000 ne ke karɓar magani a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya baiyana haka a taron manema labarai kan zagayowar ranar yaƙi da cutar sida ta duniya.

Ya baiyana cewa gwamnatin jihar ta duƙufa wajen bawa masu ɗauke da cutar magani ne domin daƙile yaɗuwar ta a jihar.

Ya kuma baiyana cewa gwamnati ta samar da cibiyoyi 600 domin lura da mata masu juna biyu da ke ɗauke da cutar don gudun ka da su yaɗawa jaririn da ke cikinsu.