
A ranar talata 28 ga watan Nuwamba aka rantsar da Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa karo na biyu. A lokacin d yake jawabi bayan ya sha rantsuwar kama aiki, Mista Kenyatta yace zai yi Gwamnati a bude wadda zata kunshi ‘yan hamayya da suke fatan cigaban kasar Kenya.
Shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto, zasu sake yin wa’adi na biyu kuma na karshe na tsawon Shekaru biyar a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa. A jawaban da ya gabatar dai bai yi bayanin ko Gwamnati tasa zata kunshi Jagoran ‘yan Adawar kasar, Riyila Odinga ba.
Sai dai a jawaban da ya gabatar masu ratsa jiki, ya bayyana cewar, shi Shugaban kasar Kenya ne wadda ta kunshi kowa da kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, dan haka yake kira ga mutanan Kenya da su bashi hadin kai domin cin ribar ayyukan raya kasa da zai shimfidawa kasar ta Kenya.
“Zan yi Gwamnati a bude, wadda ta kunshi kowa da kowa, burinmu yanzu shi ne samar da dabarun da zasu kawowa kasar Kenya cigaba mai dorewa ba tare da la’akari da yanki ko kabila ko addini ba, kasar Kenya ta dukka ‘yan Kenya ce, babu wani wanda yafi wani sabi da kabila ko yanki ko addininsa”
Dubunnan mutane ne, dai suka halarci babban filin wasa na birnin Nairobi da aka gudanar da bikin rantsuwar, inda aka yi ta kade kade da bushe bushe a wajen filin wasa, tare da rera taken kasar, sannan kuma a gefe guda, mutane na ta daga jajayen kyallaye, alamar jam’iyyar Shugaba Kenyata.
Shugaba Kenyatta dai yana kan zagon na biyu kuma na karshe a matsayin Shugaban Kenya. Yanzu dai duniya zata zuba masa ido dan ganin yadda zai gudanar da Gwamnatinsa, kamar yadda yace zata kunshi dukkan ‘yan Kenya ba tare da la’akari da addini ko yanki ko kabila ba. Abinda ba’a sani ba shi ne, ko Gwamnati zata kunshi jagoran ‘yan hamayyar kasar Rayila Odinga?